Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Nijar

A A Ahal
0



Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Nijar



 Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Nijar

  Awanni 10 da suka gabata


  Rundunar sojin kasar ta sanar da karbar mulki a hukumance a Nijar.

  Wasu sojoji kalilan ne suka bayyana a gidan talabijin na kasar inda suka tabbatar da juyin mulkin da suka yi.

  Mai magana da yawun sojojin, Manjo Ahmadou Abdhamane ne ya sanar da juyin mulkin.

  Sun sanar da rusa kundin tsarin mulkin kasar, tare da rufe dukkan iyakokin kasar.

  Kawo yanzu dai babu labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki.

  Amma sojojin sun sanar da cewa sun tsige shi daga mukaminsa.

  Sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na tabarbarewar tsaro da tattalin arziki.

  Sun kuma sanar da kafa dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe.

👉👺Karanta 

Aambasadan Kasar Nijar a Amurka ya ce har yanzu Muhammadu Bassou ne shugaban kasa

  Shugaban kasar Benin, Patrice Talon, wanda ke jagorantar tawagar ECOWAS a kasar, amma ya kasa cimma matsaya da jami'an tsaron fadar shugaban kasar da suka karbi mulki.

  A safiyar jiya ne aka bayar da rahoton tsare shugaba Bazoum a gidan gwamnati, wanda ya kai ga zanga-zangar magoya bayan Bazoum.

  Sojojin sun yi harbe-harbe don tarwatsa masu zanga-zangar.

  Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana rashin goyon bayan kasarsa ga juyin mulkin.

  Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya tattauna da Shugaba Bazoum kuma ya tabbatar masa da cewa yana da goyon bayan Majalisar.

  Wannan dai shi ne juyin mulki na hudu a Nijar tun bayan samun ‘yancin kai daga kasar Faransa a shekarar 1960, kuma an yi yunkurin juyin mulki da dama da bai samu nasara ba a kasar.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top